x

Kwalejin Kimiyya Da Fasaha Da Jami’ar Aliko Dangote Sun Kulla Yarjejeniyar Alakar Karatu.

Must read

JABIRU HASSAN, Daga Kano.

A Tamar Litinin din data gabata, watau 29 ga watan Yuli, shekara ta 2024 Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wato Kano State Polytechnic tare da Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Aliko Dangote dake Garin Wudil suka rattaba hannu akan jarjejeniyar kulla alakar gabatar da karatun Postgraduate Diploma a bangarorin Kimiyya, Fasaha da Kuma Kere-kere.

A jawabin da ya gabatar a yayin rattaba hannun, Shugaban Jami’ar Fasaha ta Wudil, Farfesa Musa Tukur Yakasai Ya bayyana matukar Jin dadinsa ga wannan hobbasa da Kwaleji Kimiyya ta Kano ta bijiro da shi wajen ganin ta cimma mafarkin da ta dade tana yi.

Ya Kara da cewa, wannan hadaka zata samar da matukar cigaba wajen bunkasa harkokin Kere-kere a fadin Jihar Kano dama Kasa baki daya.

Farfesa Yakasai Ya jaddada cewa a yanzu Jami’arsu ta sahalewa Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, wato Kano State Polytechnic ta fara gabatar da karatun Postgraduate Diploma a fannoni guda 9, tare da tabbatar da cewa nan gaba kadan za’a Kara shigo da wasu sababbin kwasa-kwasan a wannan hadaka.

Ya kuma yabawa Shugaban Kwalejin, Dr. Abubakar Umar Farouq, FCA wajen jajircewarsa don ganin an cimma wannan nasara.

A nasa jawabin, Shugaban Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Dr. Abubakar Umar Farouq Ya bayyana matukar Jin dadinsa tare da mika godiya ga Allah da Ya nuna masa wannan rana ta saka hannun akan wannan yarjejeniya.

Ya Kara da cewa, wannan hadaka tsakanin makarantun Kimiyya da Fasaha mallakin Jihar Kano guda biyu zai matukar taimakawa kokarin da Gwamnatin Jihar Kano, karkashin Jagoranci Alhaji Abba Kabir Yusuf take wajen ganin ta bunkasa ilimi, musammam na bangaren Kimiyya da Fasaha.

Dr. Farouq Ya jaddada cewa wannan hadaka zata baiwa dumbin matasa da masu sha’awar cigaba da karatu damar cimma burikansu ba tare da wahala ba.

A karshe Ya godewa Shugaban Jami’ar ta Wudil gami da masu taimaka masa wajen ganin an cimma wannan nasara, tare da tabbatar da cewa Kwalejin Fasaha ta Kano za tayi duk Maiyiwuwa wajen ganin komai Ya tafi akan tsari.

Copyright DAYBREAK NIGERIA.

All rights reserved. This material, and other digital content on this website, may not be reproduced, published, broadcast, rewritten or redistributed in whole or in part without prior express written permission from DAYBREAK NIGERIA.

More articles

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

- Advertisement -

Latest article